Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai saka Najeriya cikin jerin ƙasashen “da ake da damuwa a kansu” saboda rahotannin da ke nuna cewa ana zaluntar mabiya addinin Kirista a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce wannan matakin shi ne “ƙaramin abu” ne da ya ɗauka domin kare ‘yancin Kiristoci a Najeriya.
“Addinin Kirista na fuskantar babbar barazana a Najeriya,” in ji shi. “Dubban Kiristoci ana kashe su, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke da alhakin hakan. Don haka na ayyana Najeriya a matsayin ƙasa dake da damuwa a kanta.”
Trump ya kuma bayyana cewa ya umarci ‘yan majalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole su fara bincike kan lamarin, tare da mika masa rahoton sakamakon bincikensu.
Sai dai a makonnin baya, wani sanata a Amurka ya yi irin wannan zargi, abin da gwamnatin Najeriya ta karyata, tana mai cewa babu wani shirin kisan gilla da ake yi wa Kiristoci a ƙasar.


