Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sanya harajin kashi 15 cikin ɗari kan shigo da man fetur da dizal zuwa Najeriya.
A cewar rahoton TheCable, amincewar ta fito ne daga wata wasiƙa mai kwanan watan Oktoba 21, 2025, wadda sakataren shugaban ƙasa, Damilotun Aderemi, ya aika zuwa ga Hukumar FIRS da NMDPRA.
Harajin zai kasance ne bisa man da ake shigo da shi, kuma an ce manufar hakan ita ce daidaita farashin shigo da mai da halin tattalin arziƙin cikin gida.
Rahoton ya ƙara da cewa aiwatar da wannan sabon haraji na iya ƙara farashin litar fetur da kimanin naira 99.72.


