Tsoron harin Boko Haram ne yasa Jonathan dakatar da cire tallafin man fetur–Sarkin Kano

0
58

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya dakatar da shirin cire tallafin mai a shekarar 2012 saboda tsoron hare-haren kunar bakin wake daga Boko Haram, ba wai zanga-zangar jama’a kaɗai ba.

Sanusi, wanda a wancan lokacin yake gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ce manufar cire tallafin ta fuskanci rashin fahimta da kuma rashin ingantaccen aiwatarwa daga gwamnati.

Ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin taron da aka yi wa take da kyakkyawan Shugabanci saboda Najeriya, kamar yadda talabijin ta Arise ta rawaito.

A cewarsa, tallafin mai da Najeriya ke kira a wancan lokaci a zahiri wani nauyi ne da gwamnati ke ɗauka.

Sanusi ya ce tsarin ya jefa gwamnati cikin asara, har ta kai ga ana bin ta bashi don biyan tallafin mai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here