Mafi yawancin shugabanni basa ƙaunar masu faɗa musu gaskiya–Sarkin Kano

0
84

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga ministoci da hadiman Shugaba Bola Tinubu da su sanya gaskiya da cigaban kasa a gaba fiye da yin biyayya da yabon shugabanni mara amfani.

Sanusi ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron ƙaddamar da wani littafi, inda shi da wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC, Atedo Peterside, suka tattauna kan tattalin arzikin Najeriya da kalubalen mulki.

A cewarsa, yawanci masu fada a ji basa son masu fadin gaskiya, suna daukar su a matsayin abokan gaba, abin da ke rage gaskiya da adalci a cikin gwamnati. Ya ce irin wannan hali na nuna son kai yana hana ci gaba.

Sarkin ya bukaci hadiman shugaban kasa da ministoci su kasance masu gaskiya da jarumta wajen ba da shawara, domin hakan ne zai taimaka wajen inganta mulki da dorewar ci gaban kasa.

Ya yaba wa gwamnatin Tinubu bisa cire tallafin mai da daidaita farashin musayar kudi, amma ya gargadi cewa nasarar wadannan matakai na bukatar tsari mai kyau da kula wajen kashe kudaden gwamnati.

A nasa bangaren, Atedo Peterside ya jaddada muhimmancin kula da kashe kudade da bin ka’idar kudi, inda su duka suka yi kira da a samu sauyi na gaskiya da gyara a cikin shugabanci domin farfado da tattalin arzikin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here