Majalisar dattawa na neman daƙile shigo da shinkafa daga ƙasashen waje

0
21

Majalisar Dattawan Najeriya ta fara yunkurin ɗaukar matakan rage kashe dala biliyan 2 da ake kashewa wajen shigo da shinkafa daga ƙasashen waje, ta hanyar kafa Majalisar Ci gaban Shinkafa ta Ƙasa wacce za ta ƙarfafa noman shinkafa a gida da kuma bunƙasa samar da abinci.

Wannan mataki na cikin kudirin dokar da sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya ya gabatar, wanda ke neman kafa majalisar da za ta daidaita bincike, sa ƙa’idoji, tallafa wa manoma, da kuma inganta kirkire-kirkire a harkar noman shinkafa.

A yayin sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudirin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda Mohammed Monguno ya wakilta, ya ce waɗannan matakai na cikin shirin sabunta kyakkyawan fata na Shugaba Bola Tinubu domin farfaɗowar tattalin arzikin ƙasa.

Akpabio ya bayyana cewa, “Dokar Majalisar Ci gaban Shinkafa ta Najeriya za ta zama ginshiƙin ƙarfafa tattalin arziki, ta samar da ayyukan yi ga miliyoyin mutane, ta rage kashe kuɗin waje wajen shigo da shinkafa, tare da mayar da Najeriya cibiyar noman shinkafa a Afirka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here