Hukumar Kula da Yanayi ta ƙasa (NiMet) ta bayyana cewa ana sa ran samun canje-canjen yanayi a wasu sassa daga Litinin zuwa Laraba, ciki har da hazo da ruwan sama.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, NiMet ta shawarci al’umma su kasance cikin shiri don fuskantar waɗannan yanayi.
Hukumar ta ce ana sa ran samun hazo mai ɗorewa har tsawon kwana uku a jihohin Borno, Yobe, Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara da kuma arewacin Kaduna.
Haka kuma, rahoton ya nuna yiwuwar ruwan sama mai haɗe da tsawa a wasu yankunan jihohin Taraba da Adamawa, yayin da ake sa ran hasken rana zai mamaye yawancin jihohin arewa ta tsakiya, sai dai akwai yiwuwar ruwan sama a Nasarawa, Kogi da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.


