Sule Lamido ya bayyana aniyar sa ta son zama shugaban jam’iyyar PDP

0
9

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana aniyarsa ta neman zama Shugaban jam’iyyar PDP a matakin ƙasa.

Lamido ya sanar da hakan ne a ranar Litinin, 27 ga Oktoba, 2025, ta shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa zai je ofishin PDP na ƙasa, dake, Abuja, domin siyan fom ɗin takara.

Ya ce: “Da ikon Allah, yau Litinin, 27 ga Oktoba, 2025, da ƙarfe 11 na safe, zan kasance a Wadata Plaza don siyan fom domin neman kujerar Shugaban jam’iyyar mu, PDP.”

Lamido, wanda tsohon Ministan Harkokin Waje ne kuma ɗaya daga cikin jigo a jam’iyyar PDP, ya nuna kwarin gwiwa cewa zai iya farfaɗo da karfin jam’iyyar tare da dawo da martabar ta.

A cewarsa, “Ƙudurina na kare dimokuraɗiyya da dawo da jam’iyyarmu ga darajarta ta asali ba zai tsaya ba.”

Ya ƙara da cewa burinsa shi ne ƙarfafa jam’iyyar PDP domin tunkarar zaɓuɓɓukan da ke tafe.

PDP dai, wacce ta mulki Najeriya daga 1999 zuwa 2015, na shirin gudanar da taron gangaminta na ƙasa domin zaɓen sabon Shugaban jam’iyyar nan gaba kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here