Ƙungiyar Likitocin Masu Neman Kwarewa ta Ƙasa (NARD) ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin gama-gari daga ranar 1 ga Nuwamba.
Sanarwar hakan ta fito ne bayan taron majalisar zartarwar Ƙungiyar na tsawon sa’o’i biyar da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban ƙungiyar, Mohammad Suleiman, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 30 da suka bai wa gwamnati domin amsa bukatunsu da har yanzu ba a cika ba.
Ƙungiyar na neman karin albashi da kaso 200 cikin 100 ga tsarin CONMESS, aiwatar da sabbin alawus-alawus da aka tsara tun watan Yuli 2022, ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya, da cire matsalolin da ke hana maye gurbin likitocin da suka bar aiki.
Suleiman ya ce an umarci shugabanni da sakatarori na cibiyoyin likitoci su gudanar da tarurrukan gaggawa domin sanar da mambobi matakan da za a ɗauka, tare da tabbatar da cikakken bin umarnin yajin aikin a fadin ƙasa.
Ya kuma zargi wasu jami’an gwamnati da na ƙungiyoyi masu zaman kansu da yin shirin cin moriyar likitocin, yana mai cewa NARD za ta tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin da muradun ta.


