Gwamnatin Kano ta soke aikin tsaftar muhalli na gobe asabar

0
10

Sanarwar da gwamnati ta fitar ta bayyana cewa an ɗage aikin saboda gudanar da bikin gargajiya na Hawan Kalankuwa da ya zo a rana ɗaya da aikin tsaftar muhallin.

Gwamnatin ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin girmamawa da kuma bayar da muhimmanci ga al’adun gargajiya a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here