Nijar ta yi ƙarin albashin da ya zarce na wata babbar ƙasar Afrika

0
12

Nijar ta yi ƙarin albashin da ya zarce na wasu manyan ƙasashen Afrika

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta amince da ƙarin mafi ƙarancin albashi daga CFA 30,000 zuwa CFA 42,000, wanda yake daidai da Naira 108,780 a Najeriya.

Matakin, wanda Majalisar Ministoci ta ɗauka a taronta na jiya Laraba, yana nufin inganta rayuwar ma’aikata da ƙarfafa su wajen gudanar da aikinsu na yau da kullum.

Gwamnatin ta ce ƙarin albashin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnati ba tare da wani bambanci ba, kuma ya biyo bayan tsadar kayan abinci da sauran bukatun rayuwa a ƙasar.

Ta ƙara da cewa wannan mataki zai rage wa ma’aikata wahala, musamman wajen biyan bukatun yau da kullum kamar abinci, sufuri da ilimin yara.

Ƙarin ya zarce Naira dubu 70,000 na mafi ƙarancin albashi da ake biya a Najeriya, duk da cewa ta zarce ne Nijar ƙarfin tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here