Ku kare kan ku daga harin ƴan bindiga, gwamnan Neja ya yi bayani a kan rashin tsaron jihar

0
10

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya ce ba zai tattauna ko biya kuɗin fansa ga ‘yan bindiga ba, yana kira ga jama’a su kare kansu daga hare-haren da ke ƙaruwa a jihar.

Yayin ziyarar Rijau da Magama, Bago ya bayyana cewa jihar na cikin “yanayin yaki”, inda ya sanar da shirin ɗaukar mambobi 10,000 na JTF don taimakawa jami’an tsaro.

Haka kuma ya haramta duk aikin hakar ma’adinai a yankin Zone C, yana mai cewa hakan ne ke taimaka wa ‘yan bindiga.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa wa waɗanda suka rasa ‘yan uwa, waɗanda suka jikkata, da kuma waɗanda suka rasa dukiyoyinsu sakamakon hare-haren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here