Jagororin PDP sun bayyana wanda zai shugabanci jam’iyyar

0
9

Shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa sun bayyana tsohon ministan harkokin musamman da hulɗa tsakanin gwamnati, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin ɗan takara don neman kujerar shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Taron da ya samar da wannan matsaya ya gudana ne a birnin Abuja da yammacin Laraba, kuma ya samu halartar fitattun jagororin PDP daga yankin Arewa, ciki har da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, Caleb Mutfwang na Plateau, Ahmadu Fintiri na Adamawa, Dauda Lawal na Zamfara, da kuma Umar Damagum, wanda shi ne shugaban jam’iyyar na ƙasa a halin yanzu.

Za a gudanar da babban taron jam’iyyar (national convention) domin zaɓar sabbin shugabannin kwamitin zartarwa na ƙasa (NWC) a ranakun 15 zuwa 16 ga Nuwamba, a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Sai dai ana ci gaba da samun ƙoƙarin da ake yi don dakatar da gudanar da taron. Wasu shugabannin PDP daga yankin kudu – Austine Nwachukwu (shugaban jam’iyya na Imo), Amah Abraham Nnanna (Abia) da Turnah George (sakatare na kudu maso kudu) – sun shigar da ƙara a kotun tarayya mai lamba FHC/ABJ/CS/2120/2025, suna neman a hana jam’iyyar ci gaba da shirin taron.

Rahotanni sun nuna cewa waɗannan masu ƙara na da alaƙa da Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, kuma suna kalubalantar sahihancin shirin taron. Kotun ta sanya ranar 31 ga Oktoba domin sauraron ƙarar.

A baya, a watan Agusta, kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na PDP ya yanke shawarar cewa tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar zai tafi Kudu, bisa tsarin da ake bi, wanda ke nufin cewa shugaban jam’iyyar ya kamata ya fito daga Arewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here