Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bayyana cewa ta dakatar da yajin aikin gargadin da ta shiga na tsawon makonni biyu domin girmama tsoma bakin manyan shugabanni da kuma ba wa Gwamnatin Tarayya lokaci domin ta cika alkawurran da suka rage tsakanin bangarorin biyu.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya sanar da hakan a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, bayan kammala taron majalisar zartarwa na ƙungiyar a safiyar Laraba.
Farfesa Piwuna ya ce dakatarwar ta biyo bayan tattaunawar da suka yi da wakilan gwamnati, musamman bayan shiga tsakani da shugabannin Majalisar Dokoki ta Ƙasa suka yi. Ya bayyana cewa kungiyar ta amince ta ba gwamnati karin wata guda domin kammala tattaunawar sabunta yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta 2009, tare da warware sauran matsalolin da ke addabar jami’o’in gwamnati.
A cewarsa: “Mun samu tattaunawa mai amfani da wakilan gwamnati kan sabunta yarjejeniyar 2009. Ba mu tsayawa a inda muka ke kafin yajin aikin ba. Gwamnati ta koma teburin tattaunawa, amma akwai sauran aiki a gaba. Don haka NEC ta yanke shawarar sake duba yajin aikin.”