Ƴan kasuwa sun tafka asara a gobarar kasuwar Alaba da ke Legas

0
16

Wani ɓangare na kasuwar Alaba da ke Legas ya kama da wuta a daren Talata, abin da ya jawo asarar dukiya mai yawa ga ƴan kasuwar.

Bidiyoyin da aka wallafa a shafin X sun nuna yadda hayaki mai yawa da harshen wuta suka tashi daga sashen da ake sayar da kujeru da kayan daki, kusa da ofishin karamar hukumar Ojo.

Wani mazaunin yankin, Ikechukwu Ude, ya bayyana cewa gobarar ta fara da kaɗan kafin ta bazu zuwa shaguna da dama.

Wasu ‘yan kasuwa da suka kasa kusantar wurin saboda tsananin wutar, sun bayyana takaicin su yayin da dukiyoyinsu ke ƙonewa a gaban idonsu.

Hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta tabbatar da faruwar lamarin.

Shakiru Amodu, daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, ya ce jami’ansu daga ofishin Ojo sun yi aiki tukuru wajen kashe gobarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here