Majalisa ta tabbatar da Naɗin Sabon shugaban Hukumar Kidaya ta Ƙasa

0
60

Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Aminu Yusuf daga Jihar Neja a matsayin shugaban Hukumar Kidaya ta Ƙasa (NPC).

Haka kuma majalisar ta amince da nadin Joseph Haruna Kigbu daga Jihar Nasarawa da Tonga Betara Bularafa daga Jihar Yobe a matsayin kwamishinoni na hukumar.

Wannan mataki na majalisar ya biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Shaidar Ƙasa da Kidayar Ƙasa, karkashin jagorancin Sanata Victor Umeh daga mazabar Anambra ta Tsakiya.

A cewar Sanata Umeh, kwamitin ya gudanar da cikakkiyar tantancewa kan dukkan waɗanda aka ba da sunayensu, inda ba a samu wani ƙorafi ko laifi a kansu ba. Ya ce sun gabatar da takardun da suka haɗa da CV, takardar wanke suna daga hukumar yaƙi da cin hanci, rahoton ‘yan sanda da kuma na DSS, kafin tantancewa ta karshe.

Bayan gabatar da rahoton, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya jagoranci mambobin wajen jefa ƙuri’a, inda yawancin mambobi suka amince da su ta hanyar kuri’ar murya.

Tun a ranar 31 ga Yuli, 2025, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya aika da wasiƙar neman tabbatar da waɗannan nade-nade ga majalisar, wacce aka karanta a zauren Majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here