An gurfanar da wata mata mai suna Aisha Ibrahim Na’ibawa a gaban wata kotun jihar Kano bisa zargin bata sunan wani jami’in ɗan sanda, inda ake tuhumar ta da cewa ta yada labarin cewa jami’in yana neman maza da kuma shan miyagun kwayoyi.
Lauyan gwamnati, Barrister Awaisu Sani Lawan, ne ya karanto takardar tuhumar da ake yiwa matar a gaban kotu, sai dai Aisha ta musanta zargin gaba ɗaya.
Bayan haka, lauyanta Barrister Aminu Nura ya roƙi kotu da ta bayar da ita beli bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙasa, sai dai kotun ta ce za ta bayyana matsayinta kan roƙon neman belin a ranar 23 ga watan Oktoba.
A halin yanzu, kotu ta umarci a tura Aisha Ibrahim Na’ibawa, gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan bukatar belin.


