Bello Turji Ya Saki Mutane Sama da 100 da Yayi Garkuwa Dasu a Zamfara

0
9

Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya saki mutane sama da 100 da ya yi garkuwa da su a Jihar Zamfara, a wani sabon yunƙuri na samar da zaman lafiya tsakanin sa da al’umma.

Wannan mataki na zuwa ne bayan tattaunawa da shugabannin al’umma a ƙarƙashin shirin North West Operation Safe Corridor, wanda ke neman kawo ƙarshen hare-hare da satar mutane a yankin.

Wannan labari ya fito daga wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makamai, wanda ya bayyana cewa waɗanda aka saki sun haɗar da maza, mata da yara, kuma an mika su ga hukumomin yankin Zamfara, sannan aka kai su asibiti don duba lafiyarsu kafin a mayar da su wurin iyalansu.

Wasu rahotanni sun ce an samu yarjejeniya tsakanin Turji da wasu malamai na addini a Zamfara kafin sakin mutanen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here