Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da amfani da littattafan Leading in a Storm da Beneath the Surface na Dr. Dakuku Peterside a matsayin kayan horo ga jami’an gwamnati domin inganta shugabanci da ayyukan gwamnati.
Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, wanda ya wakilci Gwamna Dikko Umaru Radda a taron kaddamar da littattafan a Abuja, ya ce littattafan na ɗauke da dabarun shugabanci da suka dace da tsarin gyaran gwamnati, musamman a fannonin tsaro, ilimi, kiwon lafiya da noma.
Gwamnatin ta sayi kwafi 500 na Leading in a Storm domin raba wa manyan jami’an gwamnati, da nufin amfani da su wajen ƙara inganta gudanarwa da bayar da sakamako mai kyau ga al’umma.