Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Aliyu Hussaini da Amir Zakariyya bisa laifin kashe malamin Jami’ar Northwest Kano, Buhari Imam, a shekarar 2016.
Mai shari’a Fatima Adamu ta ce kotu ta tabbatar da cewa sun kai wa malamin hari a gidansa a Sheka, suka sace wayarsa sannan suka soka masa wuka har ya mutu.
Kotun ta yanke musu shekaru biyar a gidan yari kan hada baki, shekaru goma kan fashi da makami, sannan hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kisan kai.
Lauyan gwamnati, Lamido Abba-Sorondinki, ya tabbatar da cewa hujjojin gwamnati sun tabbatar da laifin waɗanda ake zargi, yayin da kotu ta ki amincewa da rokon sassauci daga lauyansu.