‘Yan sanda a jihar Kano sun sako ɗan jarida Ishaq Dan’uwa Rano bayan da aka janye korafin da aka shigar a kansa.
Rahotonni sun nuna cewa bangaren hadimin gwamnan Kano ne suka janye ƙorafin da suka kai wa ‘yan sanda akan ɗan jaridar.
Tun da farko, an kama ɗan jaridar ne bisa wani rahoto da ya wallafa da ke da alaƙa da zargin badakalar naira biliyan 6.5 da ake zargin Daraktan Hukumar Kula da Al’amuran Fada (DG Protocol) na Gwamna Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Rogo.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan janyewar ƙorafin, ‘yan sanda suka sako ɗan jaridar ba tare da wani sharaɗi ba.