Shin da gaske ne sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Najeriya ?

0
8

Shin da gaske ne sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Najeriya ?

Rrahotanni sun nuna cewa an tsare wasu manyan hafsoshin soji bisa zargin shirin yin juyin mulki a kan gwamnati mai ci ta shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cewar rahotanni daga wasu kafafen labarai kamar Sahara Reporters, akalla janar ɗaya da wasu jami’an soja 15 daga mukamin kyaftin zuwa birgediya janar ne hukumar leken asiri ta sojoji (Defence Intelligence Agency – DIA) ta kama bisa zargin cewa suna shirin kifar da gwamnati.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa tana cewa ba juyin mulki ake shirin yi ba, illa dai an kama wasu jami’an saboda saba ƙa’idojin aiki da rashin ladabi a cikin rundunar, ciki har da gazawa a jarabawar karin girma.

A halin yanzu babu cikakken tabbaci daga hukumomi cewa an shirya wani juyin mulki na gaske, domin bincike yana ci gaba da gudana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here