An bayyana ƙasar da ministan kuɗi ya tafi domin yin jinya

0
13

Ministan Kudi kuma Mai Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Najeriya, Wale Edun, ya tafi ƙasar Birtaniya domin neman lafiya, kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar a safiyar Talata.

Rahoton da jaridar Western Post ta fara wallafawa ya tabbatar da cewa ministan ya yanke shawarar tafiya ƙetare domin duba lafiyarsa, bayan wata majiya daga ma’aikatar kuɗi ya bayyana cewa akwai yiwuwar hakan idan bukata ta taso.

Majiyar ta tabbatar cewa, “Eh, gaskiya ne, ya riga ya tafi Burtaniya.”

Rahotanni sun nuna cewa Edun ya bar Abuja zuwa Legas da yammacin Litinin ta jirgi kafin daga bisani ya tafi Birtaniya.

Daga bisani, ya tashi zuwa Landan a jirgin British Airways da daddare.

Kafin tafiyarsa, wasu jami’an fadar shugaban ƙasa da suka tattauna da wakilin jaridar Punch, a ranar Lahadi sun tabbatar da cewa Edun yana jinya a gidansa da ke Abuja, ƙarƙashin kulawar likitoci.

Majiyoyin sun bayyana cewa ministan ya yi rashin lafiya a ‘yan kwanakin baya, amma sun karyata jita-jitar da ke cewa ya samu shanyewar ɓarin jiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here