Ana samun karin jita-jita cewa Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, na dab da barin jam’iyyarsa ta PDP domin komawa jam’iyyar APC, kwanaki bayan Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya yi irin wannan sauyi.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin na kusa da gwamnan sun fara tattaunawa da shugabannin APC a matakin jiha, inda wasu matasa suka gudanar da zanga-zangar maraba da shi a Jalingo, suna kira gare shi da ya sauya sheka.
Gwamnan ya kafa kwamiti ƙarƙashin tsohon Sanata Dahiru Bako domin jin ra’ayin jama’a kafin ya yanke hukunci.
Sai dai wannan yunkuri ya haifar da fargaba a cikin APC reshen jihar Taraba, musamman daga ‘yan siyasar da ke da buri na takara a 2027, suna ganin shigowar Kefas da manyan ‘yan PDP zai iya rage musu dama.
Tun bayan da Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya koma APC tare da yawancin masu rike da mukamai na PDP a jiharsa, jam’iyyar APC ta kara samun karfi a kudu maso gabas. Haka kuma, gwamnoni na Delta da Akwa Ibom sun riga sun koma APC tun farkon shekarar nan.
Ana kuma rade-radin cewa gwamnonin Bayelsa, Douye Diri, da na Zamfara, Dauda Lawal, na iya bin sawun su, duk da cewa sun musanta hakan a bainar jama’a.
Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa wannan guguwa ta sauya sheka na nuna raunin akida da gaza cika alƙawura a tsakanin jam’iyyun Najeriya. Wasu kuma sun yi gargadin cewa hakan na iya kai kasar ga zama mai jam’iyya ɗaya, abin da zai cutar da dimokuradiyya.