Ghana ta koro ’yan Najeriya 16 kan damfara ta intanet

0
102

Hukumomin kasar Ghana sun koro wasu matasa ’yan Najeriya 16 kan laifukan damfarar mutane ta intanet a kasar.

Hukumar Kwastam ta Najeriya, Reshen Seme da ke Jihar Legas, Chukwu Emeka, ya ce yawancin ’yan Najeriyyar da Ghana ta koruo matasa ne, da ke ikirarin cewa yaudarar su aka yi, ko kuma da kansu suka bar Najeriya domin samun ci gaban rayuwa.

“Hukumar Binciken Hadahdar Kudade ta Kasar Ghana na zargin su da aikata damfara ta intanet, amma binciken sharar fage da muka yi ya nuna wasunsu yaudarar su aka yi suka fara mummunar harkar, matsalar da matasanmu ke da ita ta neman yin arziki far daya.

“Wasu daga cikinsu an yaudare su ne cewa za su samu arziki idan suka bar Najeriya, amma da suka isa Ghana sai suka ga ba haka abin yake ba.

“Bincikenmu ya nuna yawancinsu sun bar Najeriya ne ta haramtacciyar hanya ta teku, wasu kuma ta wasu kasashen Afirka,” in ji shi.

Kwanturolan Kwastam din ya bayyana takaicin ganin matasan Najeriya na aikata miyagun ayyuka maimakon bunkasa basirar da Allah Ya yi musu domin ta amfane su a nan gaba.

Jami’in ya urge ’yan Najeriya da su rika bin hanyoyi tare da mallakar takardun da suka dace a duk lokacin da za su yi tafiya, sannan su tabbata halastattun harkoki suke yi na neman kudi.