Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce wahalar tattalin arzikin da ’yan ƙasa ke fama da ita za ta ƙare nan gaba kaɗan, domin Najeriya na shiga sabon mataki na bunƙasar cigaba.
Yayin wani taro a Abuja kan cigaban amfani da makamashi mafi dacewa ga muhalli Shettima ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu yana jin raɗaɗin halin da talakawa ke ciki, kuma gwamnati na aiki tukuru don kawo sauƙi.
Ya bayyana cewa Najeriya na da damar samun manyan jarin da za su samar da ayyukan yi fiye da dubu ɗaya da ɗari biyar a faɗin ƙasa, musamman ta fannin makamashi mai tsafta.
A cewarsa, burin gwamnati shi ne ta kafa Najeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi a Afirka, tare da tabbatar da cewa kayayyakin da za a rika amfani da su, an sarrafa su ne a cikin ƙasa.