Hukumar kula da gasar Premier ta Najeriya (NPFL) ta sake cin tarar ƙungiyar Kano Pillars FC bayan tashin hankali da ya barke a wasa tsakaninta da Shooting Stars FC a ranar 12 ga Oktoba, 2025.
Sabuwar tarar ta kai Naira miliyan 9.5, wanda hakan ya kai jimillar tarar da aka ci ƙungiyar a cikin shekara shida zuwa sama da Naira miliyan 46.
A cewar sanarwar da NPFL ta fitar a ranar 13 ga Oktoba, an samu Kano Pillars da laifin karya ƙa’idojin gasar bayan magoya bayanta sun mamaye fili, suka kai hari ga ‘yan wasa da jami’an wasa a filin Sani Abacha dake Kano.
Hukumar ta bayyana lamarin a matsayin “mummunan take hakkin tsaro da rashin ɗabi’a ta wasanni,” tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da yaki da tashin hankali a filayen kwallon kafa na ƙasar.
Baya ga tarar kuɗi, NPFL ta kuma cire wa Pillars maki uku da ƙwallaye uku, sannan ta rufe filin wasa na Sani Abacha har a gama wannan kakar wasanni ko aƙalla wasanni goma inda aka matsar da wasanninsu zuwa Katsina. An kuma umurci ƙungiyar da ta gano masu laifin ta shigar da su kotu, tare da gabatar da sabon tsarin tsaro cikin kwanaki bakwai.