Trump zai duba yiwuwar amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu

0
8

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai yi nazari tare da yin shawara kan abin da ya dace game da yiwuwar amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya ce zai yi aiki tare da ƙasashen duniya wajen neman mafita ga rikicin yankin, inda ya bayyana hakan yayin da yake hira da manema labarai a kan hanyarsa ta dawowa daga ziyarar da ya kai Gabas ta Tsakiya, domin sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Gaza.

A kwanakin nan, ƙasashe da dama na duniya suna ƙara matsa lamba kan batun amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu, musamman bayan babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a Amurka.

A yayin jawabin Trump a majalisar dokokin Isra’ila ranar Litinin, wani ɗan majalisa ya nemi shugaban ya goyi bayan kafuwar ƙasar Falasɗinu abin da ya jawo jami’an tsaro suka fitar da ɗan majalisar daga zauren nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here