Jam’iyyar adawa ta fara samun rinjaye a sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kamaru

0
27

Sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasa a Kamaru ya nuna cewa dan takarar jam’iyar adawa Issa Tchiroma Bakary na samun gagarumar nasara a wuraren da aka saba ganin tsohon shugaban kasa Paul Biya na da rinjaye a lokacin zaɓe.

Biya, mai shekaru 92, na fafatawa da wasu ‘yan takara tara ciki har da tsoffin ministocinsa. Rahotanni daga Yaoundé sun nuna jam’iyyar FSNC ta Bakary na samun karbuwa sosai kan jam’iyyar CPDM ta Biya.

Bakary, wanda ya fito daga yankin Far North, ya kuma fi kuri’u a yankin nasu da Bello Bouba Maigari. Sai dai ana sa ran Biya zai samu goyon baya a yankunan Kudu maso yamma da arewa maso yamma.

Duk da ci gaban Bakary, sakamakon bai zama na karshe ba har sai Majalisar Tsarin Mulki ta tabbatar da shi cikin makonni biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here