Ƙungiyar malaman jami’a ta CONUA ta bayyana cewa ba ta cikin yajin aikin da kungiyar ASUU ta fara a fadin ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Niyi Sunmonu, ya ce CONUA tana bin hanyar tattaunawa da gwamnati ba yajin aiki ba, domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba a jami’o’in Najeriya.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta nemi a saka ta cikin kwamitin da ke nazarin yarjejeniyar 2009, kuma yanzu ma’aikatar ilimi ta amince da hakan.
Sunmonu ya roƙi mambobin CONUA su ci gaba da aiki, sannan ya shawarci ɗalibai su ma su mai da hankali a kan karatunsu.
An kafa CONUA a 2018 a matsayin ƙungiyar da ta balle daga ASUU, wadda ke adawa da amfani da yajin aiki a matsayin hanyar neman hakkokin ma’aikatan jami’a.


