An kama mutumin da ya sayar da ɗansa kan Naira miliyan 1.5

0
50

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan ƙaramar hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kacal kan Naira miliyan ɗaya da rabi (₦1.5m).

Rahotanni sun bayyana cewa Onwe ya sayar da jaririn ne ga wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje.

Majiyar rundunar ta ce matar Onwe, Philomena Iroko, ce ta fallasa mijinta bayan ta ji daga maƙwabta cewa ya sayar da jaririn da suka haifa.

Bayan ta tabbatar da gaskiyar maganar, sai ta garzaya ofishin ’yan sanda inda aka kama Onwe ba tare da ɓata lokaci ba.

Kakakin rundunar jihar, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da cewa an ceto jaririn daga hannun wacce ta saya, sannan an kama ta, domin ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here