Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi da afuwa ga Maryam Sanda, wadda aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Maryam Sanda, mai shekaru 37, ta shafe fiye da shekaru shida a gidan gyaran hali na Suleja kafin samun wannan afuwa daga fadar shugaban kasa.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa wannan mataki ya zo ne bisa shawarar kwamitin da ke duba batun yafewa masu laifi a Najeriya.