Majalisa ta fara binciken NNPC akan Dala biliyan 18 na gyara matatun fetur

0
24

Majalisar Wakilai ta amince da fara bincike kan dalilin da yasa matatun mai na gwamnati, Port Harcourt, Warri da Kaduna, suka gaza aiki duk da cewa an kashe fiye da dala biliyan 18 wajen gyaransu cikin shekaru 20 da suka gabata.

Wannan mataki ya biyo bayan kudurin da dan majalisar, Sesi Oluwaseun Whingan, ya gabatar a zaman majalisar da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Whingan ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da yin alkawuran gyara matatun, amma babu wani ci gaba da ake gani, abin da ya sanya Najeriya ke dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje.

Ya tunatar da cewa a shekarar 2007, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sayar da matatun ga Alhaji Aliko Dangote da wasu masu zuba jari, amma daga baya tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua ya soke sayarwar, inda gwamnati ta dauki nauyin gyaransu da kanta, abin da bai haifar da wani sakamako mai kyau ba.

Lamarin ya sake janyo hankalin jama’a bayan Dangote da Obasanjo sun bayyana cewa matatun ba su da amfani, kuma kudin da aka kashe wajen gyaransu bata lokaci da asarar dukiyar kasa ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here