Fadar Shugaban Ƙasa ta karyata rahoton da Bankin Duniya ta fitar, wanda ya bayyana cewa mutane miliyan 139 ne ke rayuwa cikin talauci a Najeriya, tana mai cewa ƙididdigar ba ta nuna ainihin halin da ƙasar ke ciki ba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Sunday Dare, ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Bankin Duniya ta yi amfani da ƙa’idar duniya da ta ɗauki duk wanda ke samun ƙasa da dala $2.15 a rana a matsayin talaka.
Fadar ta bayyana cewa wannan ƙa’ida an kafa ta tun a shekarar 2017, kuma idan aka fassara ta zuwa kuɗin Najeriya a yau, ta kai kusan Naira 100,000 a wata fiye da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da gwamnati ta amince da shi.
A cewar sanarwar, bayanan da Bankin Duniya ya dogara da su sun fito ne tun daga shekarun 2018 zuwa 2019, wanda ke nufin ba su haɗa da sauye-sauyen tattalin arzikin yanzu ba.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce, abin da ya fi muhimmanci shi ne matakan da ake ɗauka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, ciki har da shirye-shirye na tallafin kuɗi ga talakawa, da bashin karatu na ɗalibai, da sauran tsare-tsare na rage raɗaɗin tattalin arziki.
Sai dai Bankin Duniya ya jaddada a rahotonta cewa duk da irin waɗannan sauye-sauyen da ake yi, talauci bai ragu ba a Najeriya.


