Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta bayyana cewa kamfanonin rarraba wuta (DisCos) a Najeriya sun yi asarar Naira biliyan 358 cikin watanni uku na zangon biyu na shekarar 2025.
A cewar rahoton NERC, DisCos sun karɓi Naira biliyan 546.71 daga hannun masu amfani da wuta, amma hakan bai kai kashi 60 cikin 100 na wutar da aka karɓo daga babban turken lantarki na ƙasa ba, saboda matsalolin rashin inganci da kuma rashin biyan kuɗin lantarki daga jama’a.
Hukumar ta kuma ce gwamnatin tarayya ta biya tallafin wuta na Naira biliyan 514.35 ga kamfanonin samar da wuta (GenCos), yayin da sama da kashi 60 cikin 100 na tashoshin samar da wuta ba su yi aiki yadda ya kamata ba.
Masani kan harkar wuta, Lanre Elatuyi, ya gargadi cewa idan ba a ɗauki mataki kan waɗannan kamfanoni ba, za a ci gaba da fuskantar asarar kuɗi da taruwar bashi a fannin wutar lantarki.