IBB ya kaddamar da ginin asibiti a garin iyayen sa dake Kano

0
32

Tsohon Shugaban Ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd) ya kaddamar da ginin sabon asibiti a garin Kumurya da ke ƙaramar hukumar Bunkure ta Jihar Kano.

An gudanar da bikin kaddamarwar a ranar Lahadi, inda tsohon shugaban ya samu wakilcin tsohon hafsan leken asirin tsaro na ƙasa, Birgediya Janar Halliru Akilu (rtd).

Janar Akilu ya bayyana cewa Babangida ba zai taɓa mantawa da garin iyayensa ba, yana mai tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafa wa al’ummar Kumurya ta fannoni daban-daban.

Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Isa Umar, ya gode wa Babangida bisa wannan muhimmin aiki, yana mai cewa asibitin zai taimaka sosai wajen ceton rayukan mutane da dama.

Haka zalika, ya yaba da rawar da Sheikh Ibrahim Khalil ya taka wajen tabbatar da cewa aikin ya tabbata.

Wani mazaunin garin, Mallam Salihu, ya bayyana farin cikinsa tare da yin addu’ar Allah ya saka wa tsohon shugaban ƙasar da alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here