Kwamishinan shari’a kuma Babban Lauyan Jihar Kano, AbdulKarim Maude (SAN), ya bayyana cewa kin halartar rundunar ’yan sanda a bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yanci ya haifar da barazana ga tsaron jihar da tayar da hankali tsakanin jama’a.
Maude ya zargi kwamishinan ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, da yin abin da ya sabawa tsarin mulki ta hanyar raina ikon da aka dora wa Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na Babban Jami’in Tsaron Jihar Kano.
A ranar bikin ’yancin kai da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Gwamna Yusuf ya bayyana rashin amincewarsa da Kwamishina Bakori tare da neman a sauke shi daga jihar Kano saboda kin shiga jerin gwano na bikin tare da jami’ansa.
Yayin da yake mayar da martani kan lamarin, Maude ya ce wannan mataki na kwamishinan ya tauye ikon zartarwa na gwamna, tare da barinsa cikin hadarin tsaro.
Ya tuna cewa bisa ga doka, kwamishinan ’yan sanda dole ne ya bi umarnin gwamna a lamurran da suka shafi tsaro da daidaiton jama’a, sai dai idan akwai wani umarni na musamman daga shugaban ƙasa.
Maude ya bayyana cewa Bakori ya gaza cika nauyin da ke wuyansa a matsayin wanda ke da alaka ta doka da amana tsakaninsa da Gwamna da kuma Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa.
Ya kara da cewa, sashe na 214 (4) na kundin tsarin mulki ya tabbatar da cewa rundunar ’yan sanda hukuma ce ɗaya ta ƙasa, amma sashe na 215 kuma ya ba gwamna damar bayar da umarnin da suka shafi tsaron jama’a a jiharsa.