Yadda Sonny Echono Ya Sauya Fusalin Makarantun Gaba da Sakandare a Najeriya

0
38

Tun bayan da Arc. Sonny Echono ya karɓi jagorancin Hukumar Tallafawa Makarantun Gaba da Sakandare ta Ƙasa (TETFund) a watan Maris na shekarar 2022, ya fara wani gagarumin shirin sauya tsarin yadda ake tallafawa manyan makarantu a Najeriya.

Echono, wanda tsohon mai zanen taswirar gurare ne kuma yanzu babban jami’i a harkar ilimi, ya ƙaddamar da sauye-sauyen zamani da suka ta’allaka da cikakken amfani da fasahar zamani da kuma gaskiya a gudanarwa, abin da ya kawo babban sauyi a yadda jami’o’i, kwalejojin ilimi da na fasaha sama da 170 ke samun tallafin gwamnati.

A ƙarƙashin jagorancinsa, TETFund ta tara harajin ilimi da ya kai naira tiriliyan 1.5 a shekarar 2024, wanda ya zama mafi girma a tarihin hukumar. Daga shekarar 2011 zuwa 2024, hukumar ta rarraba sama da naira tiriliyan 1.8 ga cibiyoyin ilimi daban-daban.

Sauye-sauye ta hanyar amfani da fasahar zamani

A zamaninsa, an canja tsarin aiki daga takardu zuwa na’ura mai kwakwalwa, inda ake yin duk wasu aikace-aikace ta intanet. 

Tallafawa Bincike da Haɗin Gwiwa

Echono ya fadada tallafin bincike musamman kan batutuwan ci gaban ƙasa kamar makamashi mai sabuntawa, sauyin yanayi da kirkire-kirkiren kiwon lafiya. Haka kuma, ya ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’o’in Najeriya da na ƙasashen waje domin haɓaka binciken kimiyya.

Martani kan Zarge-Zargen Cin Hanci

A watan Afrilu 2024, Echono ya fuskanci zarge-zargen cin hanci, amma ya musanta hakan da cewa, “zarge-zargen sun yi tsanani fiye da gaskiya.” Hukumar HEDA ta nemi hukumar ICPC ta binciki al’amuran hukumar domin tabbatar da gaskiya.

Duk da haka, Echono ya ci gaba da samun yabo daga ƙungiyoyi daban-daban, ciki har da lambar yabo ta “Outstanding Public Servant of the Year” daga jaridar Champion Newspapers a watan Yuli 2024.

Tsaurara Kulawa da Ayyuka

A karkashin sabon tsarin sa, TETFund ta kafa ingantattun matakai na lura da ayyuka, inda kwangiloli ke fuskantar tsauraran sharudda kafin kammalawa.

Ƙarfafa Matasa da Ƙirƙirar Ayyukan Yi

Domin magance matsalar rashin aikin yi, TETFund ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa sana’o’i da kirkire-kirkire, don taimaka wa matasa su daina dogaro da neman aiki kawai, su fara ƙirƙirar nasu.

A ƙarshe, sauyin da Echono ya kawo a TETFund na nuna sabuwar hanya ta inganta gudanarwa, gaskiya, da amfanar da kuɗin gwamnati a fannin ilimi, abin da zai iya zama ginshiƙi wajen gina tsarin manyan makarantu masu inganci a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here