Tinubu zai halarci binne gawar mahaifiyar shugaban APC

0
46

Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, zai kai ziyara a jihar Filato gobe Asabar domin halartar jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantawe Yilwatda.

Bisa bayanin da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu zai yi jawabi ga manyan jagororin addinin Kirista a wata coci dake birnin Jos.

Rahoton ya ƙara da cewa shugaban zai isa jihar, ya halarci jana’izar tare da gudanar da sauran shirye-shiryen da aka tanada, sannan ya koma fadar Aso Rock a goben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here