Tinubu Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Daina Yi Wa Ƙasar Mummunan Fata

0
50
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su daina yin magana ko fata marar kyau ga ƙasar, yana mai jaddada cewa Najeriya ƙasa ce mai girma wacce ke cike da albarkatu masu yawa.

Tinubu ya yi wannan jawabi ne a daren Talata a Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) bayan an gyara ta.

A cewarsa, ya zama dole ’yan ƙasa su haɗa kai domin gina Najeriya tare da nuna alfahari da ita.

> “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu jajircewa da alfahari. Mu gina wannan ƙasa tare, mu farfaɗo da ita,” in ji Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here