Rashin tsaro ya sa an rufe makarantun Boko kusan 200 a Arewa–Bincike

0
45

Rashin tsaro ya sa an rufe makarantun Boko kusan 200 a Arewa–Bincike

Rahotanni sun tabbatar da cewa makarantu akalla 188 aka rufe a jihohin Arewa saboda matsalolin tsaro, musamman hare-haren ‘yan bindiga da ƙungiyoyin ta’addanci.

A wani binciken da aka gudanar, an gano cewa a Zamfara makarantu 39 sun rufe, a Katsina 52, a Benue 55, a Niger 30, yayin da Sokoto da Kaduna suka rasa akalla 6 kowanne. Wasu daga cikin waɗannan makarantu an mayar da su sansanonin ‘yan gudun hijira ko kuma wurin zama ga jami’an tsaro.

Jihohin da suka fi fuskantar matsalar sun haɗa da Zamfara, Katsina, Niger, Kaduna, Sokoto, Kebbi da Benue. A wasu ƙauyuka, gaba ɗaya al’umma sun tsere, makarantu kuwa sun zama na banza.

Hakan ya tilasta dubban yara sun daina zuwa makaranta, wasu kuma an tura su birane domin ci gaba da karatu a cikin ajin da ya cika. Sai dai wasu sun daina gaba ɗaya

Kididdiga daga UNICEF ta nuna cewa Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya, inda yara kusan miliyan 18 ke zaune a gida ba tare da samun ilimin boko ba.

Masanan ilimi sun yi gargadin cewa tsawon lokacin da makarantu za su ci gaba da zama a rufe, hakan zai ƙara haifar da jahilci da fatara, tare da tunzura matasa ga aikata laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here