Tinubu da Sarkin Kano sun kaddamar da cibiyar Wole Soyinka a Lagos

0
49

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II sun kaddamar da sabuwar cibiyar al’adu da kirkira mai suna Wole Soyinka Centre for Culture and the Creative Arts, a Iganmu, Lagos.

A wajen taron an samu halartar fitattun mutane ciki har da Matar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu; Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu; Farfesa Wole Soyinka; Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila da Ministar Al’adu Hannatu Musawa.

Wannan aiki, a cewar shugabannin, zai taimaka wajen bunkasa harkokin al’adu, fasaha da kirkira a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here