Gwamnatin Jihar Kano ta hannun Majalisar Shura ta dakatar da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawan Shuaibu Triumph, daga gudanar da wa’azi har sai an kammala bincike a kansa.
Sakataren Majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Laraba. Ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin bai wa malamin damar bayyana kansa kan zargin yin maganganu da ake ganin suna tozarci ga Annabi (SAW).
Sagagi ya ce, Sheikh Lawan zai ci gaba da kasancewa a karkashin dakatarwa har sai an saurari kariyarsa kuma an kammala bincike.
Haka kuma, ya yi gargadi ga ‘yan siyasa da su guji tsoma baki cikin lamarin, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da binciken cikin adalci da gaskiya ba tare da nuna son kai ba.