Sojoji sun kama ƴan sandan bogi da motar tabar wiwi

0
85
Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Brigade ta 6 tare da jami’an NDLEA sun kama wasu mutane biyu da suka yi amfani da kayan ƴan sanda tare da motoci biyu cike da tabar wiwi a Wukari, jihar Taraba.

Bayanin da aka fitar ranar Laraba daga Lt. Umar Muhammad, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ya ce an cafke su ne a Takum Junction, bayan samun sahihan bayanan sirri.

An gano cewa mutanen ba jami’an tsaro ba ne, kuma motoci nau’in Toyota Hilux ɗin da ke ɗauke da kayan an ɗebo su ne daga Akure, jihar Ondo, suna kan hanyarsu zuwa Adamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here