Wani malamin Musulunci a Najeriya, Dr. Sharafudeen Gbadebo, ya gargadi ma’auratan Musulmi da su guji yin gwajin DNA wajen tabbatar da nasabar su yaran da suka haifa, yana mai cewa hakan bai halatta ba a cikin Musulunci.
Ya bayyana cewa addini ya riga ya tanadi tsarin Li’ani, inda miji da mata ke yin rantsuwa a gaban Alkalai, idan aka samu shakku kan asalin mahaifin yaro, kuma hakan ne kadai hanyar da Musulunci ya amince da ita.
Sai dai wata masaniyar harkar lafiya, Aisha Ahmad daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin, ta ce gwajin DNA na da inganci sama da kashi 99% wajen gano ainihin iyaye, duk da cewa ba zai iya halatta ɗa na zina a Musulunci ba.


