Matatar Dangote zata dawo da ma’aikatan da ta kora daga aiki

0
62
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Matatar Dangote ta amince da sake ɗaukar ma’aikatan da ta kora bayan wani zaman sasanci da aka gudanar tsakanin jagororin matatar da ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN.

A wata sanarwa da ma’aikatar ƙwadago ta fitar ranar Laraba, an bayyana cewa ma’aikatan da aka sallama za a mayar da su cikin sauran rassan kamfanin ba tare da rage musu albashi ba.

Ministan ƙwadago da ayyuka, Mohammed Dingyadi, ya bayyana cewa ‘yancin ma’aikata na shiga ƙungiya ya tabbata a ƙarƙashin dokokin Najeriya, don haka dole ne a mutunta hakan.

Haka kuma, an cimma matsaya cewa babu wani ma’aikaci da za a yi wa ramuwar gayya saboda rawar da ya taka a rikicin da ya haifar da wannan matsala.

Ƙungiyar PENGASSAN ta ce za ta fara janye umarnin yajin aikin da ta ɗauka a ranar 26 ga Satumba bisa dalilin korar ma’aikatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here