Matashin Limami Ya Rasu a Hannun ’Yan Sanda a Kano

0
50

Al’ummar Kuntau a ƙaramar hukumar Gwale, Jihar Kano, sun shiga cikin jimami bayan mutuwar wani matashin limami, Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu sakamakon duka da jami’an ’yan sanda suka yi masa.

An ce an kama Salim mai shekara 24 ne a gidansa bayan ya kammala jagorantar sallar Magariba ranar 22 ga Satumba, bisa wani zargin aikata laifi.

Mahaifinsa, Sheikh Adam Usman, ya shaida cewa bidiyon CCTV ya nuna jami’ai biyu suna dukansa a lokacin da suka zo su kama shi, sannan daga baya aka ci gaba da dukansa a ofishin ’yan sanda har ya mutu.

Ya ƙara da cewa, duk da ƙoƙarinsa na ganin ɗansa a daren da aka kama shi, jami’an sun hana shi, sai daga baya aka sanar masa cewa ya rasu. Gawar tasa dai an ajiye ta a Asibitin Abdullahi Wase, bayan farko an kai ta Asibitin Murtala Muhammad a matsayin gawar “wanda ba a sani ba.”

Wata kotu ta bayar da umarni a yi masa gwajin likita a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, wanda ake sa ran sakamakonsa zai fito cikin makonni huɗu.

Mazauna unguwar sun bayyana Salim a matsayin mutum mai sauƙin kai da zaman lafiya, inda suka ce mutuwarsa ta jefa su cikin alhini.

Sai dai har yanzu rundunar ’yan sandan Kano ba ta fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here