Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta fara yajin aiki bisa korar sama da ma’aikata 800 daga Matatar Mai ta Dangote.
Sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya bayyana cewa tun daga safiyar Lahadi, mambobinsu sun daina aiki a wuraren da abin ya shafa, kuma umarnin zai shafi ofisoshi da hukumomi a duk fadin Najeriya daga daren Litinin.
Ƙungiyar ta kuma dakatar da kai ɗanyen mai da gas zuwa matatar, tare da buƙatar a dawo da dukkanin ma’aikatan da aka kora.
A nasa martanin, kamfanin Dangote ya ce korar “’yan kaɗan ne abin ya shafa” a matsayin wani ɓangare na sake tsara harkokinsa, sai dai PENGASSAN ta ce hakan rashin adalci ne.


