Jami’ar Bayero dake Kano (BUK) ta tabbatar da korar dalibai 57 bisa laifin saɓa dokokin jarrabawa, tare da dakatar da wasu 8 na ɗan lokaci. Haka kuma, an wanke dalibai 2 daga zargin aikata laifi bayan bincike ya tabbatar da rashin laifinsu.
Wannan hukunci ya fito ne daga zaman majalisar zartarwar jami’ar karo na 427, bisa tanadin dokokin gudanar da jarrabawa da ƙa’idojin jami’ar.
Hukumar ta jaddada aniyar ta na ci gaba da kare martabar jarrabawa da ingancin takardun shaidar karatun jami’ar, tare da gargadin dalibai su kiyaye dokokin jarrabawa domin gujewa irin wannan hukunci a nan gaba.