Haƙurin ƴan Najeriya ya haifar da farfaɗowar tattalin arziƙin ƙasa–Tinubu

0
14

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da juriya da haƙurin ‘yan Najeriya a kan ƙalubalen tattalin arziki da na zamantakewa da ake fuskanta a yanzu. Ya ce wahalhalun da ake sha ba zasu tafi a banza ba, domin tuni suka fara haifar da ci gaba da kuma bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

Tinubu ya faɗi haka ne ranar Juma’a a wajen bikin naɗin Sarkin Ibadan na 44, Oba Rashidi Ladoja, da aka gudanar a dandalin Mapo Hall a Ibadan.

Shugaban ƙasa ya bayyana cewa koda yake rayuwa ta yi tsanani a baya-bayan nan, gwamnati na kafa tubalin makoma mai inganci wadda za ta samar da arziki da walwala ga kowa.

A yayin jawabinsa, ya kuma yaba da kwarewa da hangen nesa na sabon Olubadan, Oba Rashidi Ladoja, wanda ya ce jama’arsa na ƙauna sosai, kuma zuwansa kan karagar mulki zai kawo sabon salo na ci gaba da haɗin kai a Ibadan.

Tinubu ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da yin aiki tare da masarautu da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here