Majalisar Shura ta Jihar Kano ta gayyaci Sheikh Lawan Abubakar Triumph domin sauraron ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar a kan sa, na zargin furta kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Haka kuma, majalisar ta umarci waɗanda suka shigar da ƙorafe-ƙorafen su halarci zaman, domin a samu damar sauraron kowane ɓangare.
Sakataren majalisar kuma Kwamishinan Kasuwanci, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana wa manema labarai cewa majalisar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe guda takwas daga kungiyoyin addini da na al’umma. Ya ce majalisar za ta gayyaci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, ciki har da Malam Triumph, domin jin ta bakin kowa.
Sagagi ya kara da cewa, majalisar za ta gudanar da aikinta bisa gaskiya da adalci, tare da bai wa gwamnati shawarar da ta dace a kan al’amarin.